1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ci gaba da ɗauki ba daɗi a ƙasar Yemen

September 25, 2011

Sojojin da suka bijire wa gwamnatin Yemen sun mai da wuta kan dakarun dake biyayya ga shugaban ƙasar da suka nemi tarwatsa boren kafa demokraɗiyya.

https://p.dw.com/p/12gCn
Wasu masu adawa da gwamnatin Yemen da aka raunataHoto: dapd

Rikici ya sake ɓarkewa a babban birnin Yemen wato Sana'a. Inda tun daren jiya ake musayar wuta tsakanin sojojin da ke goyon bayan masu boren kafa mulkin demokradiyya da dakarun dake biyayya ga shugaba Abdullah Saleh, inda akalla mutane 40 suka hallaka a yunƙurin da dakarun gwamnatin ƙasar suke yi na murkushe masu neman sauyi, kana daga bisa dakarun gwamnati sun kutsa cikin garin domin murkushe wadanda ke sansanin masu zanga-zangar. To sai dai wannan bai hana masu neman sauyin gudanar da jerin gwano a sauran biranen ƙasar ba, suna kira ga shugaba Ali Abdallah Saleh ya sauka a kuma gurfanar da shi a gaban ƙuliya. Duk wannan yana faruwa ne bayan da Abdallah Saleh ya dawo daga Saudiyya inda ya je jinya bayan da masu boren suka kai wani harin bam a fadar gwamnatin sa a watan Yunin da ya gabata.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Usman Shehu Usman