An bukaci jan kunnen masu kyamar baki a Jamus
August 24, 2015Talla
'Yan majalisar dokokin tarayyar Jamus sun bukaci da a dauki tsauraran matakai kan masu shirya zanga-zangar kyamar baki musamman ma dai 'yan gudun hijira.
Wasu gungun mutane a karshen mako sun yi jerin gwano don nuna rashin amincewarsu da tsugunar da 'yan gudun hijra a garin Heidenau da ke a jihar Saxony da ke gabashin kasar.
Wata 'yar majalisar dokokin jihar ta Saxony Juliane Nagel ta danganta wannan zanga-zanga da aka yi ta kyamar 'yan gudun hijirar da rashin cikakkiyar masaniya ta girke su a jihar.
To sai dai masu adawa da wannan mataki na irin wadannan mutane sun gudanar da zanga-zanga ta lumana don yin Allah wadai da masu kyamar 'yan gudun hijirar inda suka ce su kan suna maraba da 'yan gudun hijirar.