An bude zaman taron neman lafiyar kasar Yemen a Kuwaiti
April 21, 2016A wannan Alhamis an fara taron tattaunawar neman zaman lafiyar kasar Yemen a kasar Kuwaiti, wadda Majalisar Dinkin Duniya ke daukar nauyin gudanarwa. Labaran tashoshin telebijin sun nuna bude zaman taron da aka sha dage shi saboda zargin karya yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma takaddama game da jadawalin taron. An shirya fara tattaunawar a ranar Litinin tsakanin 'yan Houthi da ke samun goyon bayan kasar Iran da gwamnatin shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi da kasar Saudiyya ke mara wa baya. Tun da farko kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya yi karin haske game da ajandar taron.
"Tawagogin za su mayar da hankali kan aiwatar da kudurin Kwamitin Sulhu mai lamba 2216. Ana sa rai za su samar da wani jadawali da zai bude hanyar aiwatar da shirin zaman lafiya karkashin shawarar majalisar hadin kan kasashen Gulf da sakamakonsa zai kai ga shirya babban taron sasanta 'yan kasa."