An bude rumfunan zabe na 'yan majalisar dokoki a Togo
April 29, 2024A bisa sauye-sauyen da 'yan majalisar suka yi wa kudin tsarin mulkin Togo, za a zabi shugaban kasa sau daya a wa'adin mulki na shekaru hudu, wanda za a iya sabunta shi sau daya, daga bisani 'yan majalisa ko kuma jam'iyyar da ke da rinjaye a majalisar dokokin kasar za ta ci gaba da nada shugaban kasa.
Karin bayani: Karar Togo kan gyara ga kundin tsarin mulki
A zaben na yau litinin al'ummar kasar ta Togo zasu zabi 'yan majalisa 113 da kuma mataimakan magadan gari 179 daga shiyyoyi biyar na kasar da kansiloli; wadanda su ke da alhakin zabar 'yan majalisar dattawan da aka kirkira a kasar.
Karin bayani: An saka ranar zabukan Togo da aka dage bayan rudanin siyasa
Shugaba Gnassingbe, ya lashe zaben shugaban kasar sau hudu da saura wa'adi daya na zaben 2025 zai kare wa'adin mulkinsa ba tare da tazarce ba, to amma wannan sabon tsarin na firaimista da 'yan majalisar dokokin kasar suka bujiro da shi zai bawa shugaban ci gaba da kasancewa kan karagar mulki har mahadi ka ture.
Karin bayani: An haramta zanga-zanga a Togo
Shugaban ya gaji mahaifinsa ne Gnassingbe Eyadema wanda ya shafe shekaru kimanin 40 yana mulkin kasar ta Togo da ke yammacin Afrika.