1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An fara kada kuri'a a zaben shugaban kasar Kwango

December 20, 2023

An fara kada kuri'a a zaben shugaban kasa na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da 'yan takara 19 ke fafatawa ciki har da shugaba mai ci Felix Tshisekedi, da ke sake neman wa'adin mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/4aN6R
Hoto: Stefan Kleinowitz/Zumapress/picture alliance

Jamhuriyar Dimukuradiyyar  Kwango na gudanar da babban zaben shugaban kasar da 'yan takara 19 ciki har da shugaba mai ci  Felix Tshisekedi, da ke sake neman wa'adin mulkin kasar da ke da dimbin arzikin ma'adinai da a gefe guda galibin al'ummar kasar ke fama da talauci.

Tshisekedi, ya hau kan karagar mulkin kasar a shekara ta 2019, a wani zabe da aka yi ta cece-kuce akan sahihancinsa da masu sanya ido na kasa-da-kasa suka yi watsi da sakamakon zaben.

Kutumbi dan shekara 58, shi ne ke kan gaba a wadanda su ke haifarwa da Tshisekedi tarnaki, kasancewar ya tare da dimbin ma magoya baya da galibinsu matasane  da ke sha'awar kwallon kafa, kuma ya taka rawar gani a lokacin da ya yi gwamna a lardin  Katanga, duk da cewa an hana shi tsayawa takara a zaben da ya gabata sakamakon zargin mallakar wasu kadarori lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Joseph Kabila.

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwang na daya daga cikin kasashe matalauta a duniya da ta ke fama da tashe-tashen hankula da yake-yake  da suka hada da  ayyukan 'yan tawayen M23 da ke gabashi da shugaba Tshisekedi ke zargin takwaransa na Rwanda, Paul Kagame, da daukar nauyin mayakan, zargin da yake ci gaba da musantawa.