1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu Amirkawa biyu sun samu lambar yabo ta Nobel

Salissou Boukari
October 8, 2018

A wannan Litinin din ce aka bayar da kyautar lambar yabo ta Nobel kan tattalin arziki ga wasu Amirkawa guda biyu da suka hada da William Nordhaus da kuma Paul Romer.

https://p.dw.com/p/36AYX
Bildkombo William D Nordhaus und Paul Romer
William D Nordhaus da kuma Paul Romer wadanda suka samu kyautar lambar yabo ta Nobel kan tattalin arziki.Hoto: imago/UPI Photo//picture-alliance/dpa/S. Thew

Paul Romer, wanda yake tsohon masanin tattalin arziki na bankin duniya da ya taka rawa wajen tsara harkokin tattalin arziki ta yadda zai yi tasiri kan yanayi. Tun dai yau da shekaru da dama wadanda suka samu kyautar sun samar da wasu dabaru da ke a matsayin mafita kan mayan kalubale da ka iya addabar yanayin da ake ciki, inda suka yi nazari kan yadda za a hada batun ci gaba mai dorewa a fannin tattalin arzikin duniya da kuma batun jin dalin al'ummar duniya. Kuma masanan biyu za su raba wannan tukuici da ya kai na kwatankwacin Euro dubu 860.

Shi dai William Nordhaus mai shekaru 77 da haihuwa, wanda Farfesa ne na jami'ar Yale, shi ne mutun na farko da ya samar da nasarin daidaita harkokin tattalin arziki da na yanayi kuma wannan kyauta da suka samu ita ce karo na 50.