An bai wa Girka mako guda kan ceto tattalin arzikin kasar
June 11, 2015Talla
Masu bayar da kudaden ceton tattalin arzikin kasar Girka sun bai wa Firaministan kasar Alexis Tsipras wa'adin mako guda ya dauki matakin rage bukatun da ya gabatar ko kuma ya fuskanci matsalolin kudi. Hukumar ba da lamuni ta duiniya, IMF ta ce muddun mahukuntan Girka ba su sauya ba, hukumar za ta janye masu tattaunawa.
An gudanar da taron a birnin Brussels na kasar Belgium, inda duk yunkurin shiga tsakani da Jean-Claude Juncker babban jami'in hukumar Tarayyar Turai ya ci tura. Bayan ranar 30 ga wannan wata na Yuni idan babu karin kudade daga kasashe masu ba da bashi, kasar ta Girka za ta cikin matsalolin rashin kudin tafiyar da lamura.