An ba da kyautar Nobel ta kimiyya
October 4, 2016Talla
An ba da kyautar Nobel ta kimiyya ga wasu 'yan kasar Birtaniya guda uku wadanda ke yin aikin bincike a Amirka.David Thouless da Duncan Haldane da kuma Michael Kosterlitz,sun samu kyautar saboda bincike da suka gudanar a game da samar da hanyoyin inganta sha'anin latronik ta hanyar lisafi mai surfi.Cibiyar Nobel Fondation da ta ba da kyautar a birnin Stockholm ta ce bincike ya taimaka sossai wajen samun ci gaba a game da sha'anin latronik da sauran abubuwa na kimiyya.