An ɗage gudanar da zaɓen gwamnoni a jihohin Kaduna da Bauchi da kwanaki biyu-INEC
April 21, 2011Shugaba Najeriya Goodluck Jonathan ya ce za a gudanar da zaɓen gwamnonin jihohin ƙasar kamar yadda aka shirya duk kuwa da tashen tashen hankulan da aka fuskanta a sassa daban daban na arewacin ƙasar bayan zaɓen shugaban ƙasa. A cikin wani jawabi da yayi shugaba Jonathan ya ce ana ci-gaba da ƙokarin maido da doka da oda da kwanciyar hankali a ƙasar, wadda ta fi kowace yawan al'uma a nahiyar Afirka. A ranar Talata mai zuwa ne za a yi zaɓen gwamnoni da na wakilan majalisun dokokin jihohin ƙasar ta Najeriya. To sai dai hukumar azɓen ƙasar mai zaman kanta ta ce ta ɗage gudanar da zaɓen a jihohin Kaduna da Bauchi ta kwanaki biyu wato zuwa ranar Alhamis, saboda rashin cikakken tsaro a jihohin.
Tuni dai ƙungiyoyin addinai da shugabannin al'uma ke yin kira da a kwantar da hankula kana a tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin jama'a. An yi kuma kira ga jama'a da su fita kaɗa ƙuri'a a lokacin zaɓukan na gwamnoni.
A ƙasa mun yi muku tanadin sautin rahotanni daban daban game da halin da ake ciki a Najeriya.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Ahmad Tijani Lawal