Amurka ta ja hankali kan takaddamar zaben Kwango
January 1, 2024Kasar Amurka ta bukaci warware takaddamar zaben Jamhuriyyar Dimokradiyar Kwango cikin lumana, biyo bayan sanar da shugaba Felix Tshisekedi, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da galibi al'ummar kasar ke fama da talauci tare da kalubalen tsaro.
A wani 'dan takaitaccen sako da ofishin ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, ta ce ta na bibiyar yadda al'amura ke gudana a kasar ta Kwango, tare kuma da bukatar dukkan bangarorin da ke adawa da sakamakon zaben da su garzaya kotun kolin kasar, don warware takaddamar cikin kwanciyar hankali.
Shugaba mai ci Felix Tshisekedi, ya lashe zaben ne da kaso 73 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada. Sannan Moise Katumbi tsohon gwamnan kana hamshakin mai arziki ya zo na biyu da kashi 18 cikin 100, kana Martin Fayulu ya kasance a matsyi na uku da kashi biyar cikin 100. Hukumar zabe ta ce an samu fitowar masu zabe na kashi 43 cikin 100.