1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka: Harris ta bukaci a tsagaita wuta a Gaza

August 23, 2024

'Yar takarar shugabancin Amurka a jam'iyyar Demokrat Kamala Harris ta goyi bayan a tsagaita wuta a yakin da ake yi a Zirin Gaza tare da bukatar sako mutanen da ake tsare da su.

https://p.dw.com/p/4joaw
Hoto: J. Scott Applewhite/dpa/AP/picture alliance

Harris ta fadi haka ne a ranar Alhamis, rana ta karshe ta babban taron jam'iyyar, daidai lokacin da ta karbi shaidar ba ta takarar jam'iyyar a hukumance. 'Yar siyasar ta ce ita da shugabanta Joe Bidenna aiki tukuru domin ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su a yakin na Gaza tare da tsagaita wuta. Ta ce ba za ta janye matsayarta kan 'yancin da Isra'ila ke da shi na kare kanta ba, amma a lokaci guda, ta fahimci girman munanan abubuwan da suka faru a yankin Gaza a watanni 10 da suka wuce. Ta ce akwai bukatar a kawo karshen wahalhalun da mutanen Gaza ke fuskanta domin mutunta 'yancinsu na darajar da suke da ita a matsayinsu na mutane da 'yancin zabar wa kansu tsarin rayuwar da suke son rayuwa a kansa.

Sama da mutum 40,000 ne ake kiyasin suka mutu a Zirin Gaza sakamakon jerin hare-haren ramuwar gayya da Isra'ila ke kai wa tun bayan harin da kungiyar Hamas ta kai mata a shekarar da ta gabata.