1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Amurka da Burtaniya da Jamus na fatan dakatar da yakin Gaza

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 6, 2024

Kasashen sun bukaci Isra'ila da Hamas da su duba tayin da idon basira, don dakatar da wannan yaki na Gaza

https://p.dw.com/p/4gjxt
Hoto: Brendan Smialowski/AFP/Getty Images

Kasashen Amurka da Burtaniya da Jamus da Canada da ma wasu kasashen, sun yi kira ga kungiyar Hamas da ta karbi tayin da shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar na kawo karshen yakin Gaza baki-daya.

Karin bayani:Gaza: Amurka ta gabatar da sabon shirin tsagaita wuta

Wata sanarwar hadin gwiwa da fadar White House ta fitar, ta ce sauran kasashen da ke goyon bayan wannan mataki sun hada da Argentina da Austria da Brazil da Bulgaria, sai Colombia da Denmark da Faransa da Poland, haka zalika akwai Portugal da Romania da Serbia da Spain da kuma Thailand.

Karin bayani:Kotu ta umarci Isra'ila ta dakatar da yaki a kudancin Gaza

Shugabannin wadannan kasashe sun bukaci Isra'ila da Hamas da lallai su duba wannan tayi da idon basira, don dakatar da wannan yaki na Gaza, wanda ke cika watanni takwas cif ana gwabzawa.