1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Inganta ayyukan bankin duniya da IMF

Binta Aliyu Zurmi
August 22, 2023

Shugaban Amurka Joe Biden zai nemi bukatar yin garanbawul ga bankin duniya da kuma asusun IMF a zauren taron kasashe masu karfin masana'antu na G7.

https://p.dw.com/p/4VSiS
USA Joe Biden Event zum Jahrestag des Inflation Reduction Act in Washington
Hoto: Kevin Lamarque/REUTERS

Biden zai yi haka ne domin lalubo hanyoyin inganta ayyukan wadannan manyan cibiyoyin bada lamuni na duniya musamman ga kasashe masu tasowa.

Taron da ke tafe a watan Satumban wannan shekara a kasar Indiya, a cewar mai bai wa shugaban Amurka shawara a kan harkokin tsaro, Juke Suullivan akwai bukatar bankin duniya da IMF su fitar da sabbin tsare-tsaren ci gaba da ma ba da lamuni cikin sauki. 

Amirka na shirin yin tayi ga Indiya na kara yawan bashin manyan cibiyoyin ya zuwa dala biliyan dubu da dari biyu.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da kungiyar Brics ke gudanar da taronta karo na 15 a kasar Afirka ta Kudu, inda kasashe sama da 40 ke rububin shiga kungiyar. Wasu na yi wa Brics kallo a matsayin wata kishiya ga kasashen yamma, sai dai Amurka ta ce bata ganinta a haka.