Amnesty ta ce a mika al-Bashir ga ICC
April 14, 2019Kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa ta Amnesty International ta yi kira a wannan Asabar ga sabbin hukumomin kasar ta Sudan da su gaggauta bayyana wurin da suke tsare da hambararren shugaban kasar Omar al-Bashir da kuma mika shi ba tare da bata lokaci ba ga kotun kasa da kasa ta ICC wacce da ma ta ba da sammacin kamoshi tun a shekara ta 2009 a bisa zargin aikata kisan kiyashi a yakin Darfour inda mutane sama da dubu 300 suka halaka wasu kimanin miliyan biyu da rabi suka rasa matsugunnansu.
Kazalika Amnesty International ta yi kira ga sabbin hukumomin rikon kwarya na kasar Sudan da su gudanar da bincike kan rawar da Salah Gosh tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar wanda ya yi murabus a jiya Asabar ya taka wajen kisan masu zanga-zanga neman sauyi a watanni hudu na baya bayan nan.