Sudan zata fita cikin zargin Amirka
July 5, 2018Talla
Matakin na Amirka ya biyo bayan matakan mastin lamba da ta yi wa Sudan na katse hula da dangantakar soji da Koriya ta Arewa. Sudan na fuskantar wariyar huladar kasuwaci da sauran kasashen dunyia bisa takunkumin karan tsaana da Amirka ta likamata da ta'addanci.
A shekarar 1997 Amirka ta shigarda Sudan cikin jerin kasahsen da ke marawa 'yan ta'adda baya, lokacin da aka zargi shugaban Al-Qaeeda Usama bin Laden na samun mafaka a kasar tsakanin shekarun 1992 zuwa 1996.
A yanzu dai Sudan na fatan Amirka ta share sunanta cikin jerin kasashen duniya ke ganin suna bawa kungiyoyin tarzoma goyon baya, matakin da zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikinta da durkushe shekara da shekaru.