Yakin Yemen na daukar sabon salo
November 10, 2018Talla
Kasar Saudiyya dai ta fara fidda sanarwar cewa a yanzu dakarunta sun kware don haka za su iya bai wa jiragensu mai a sararin samaniya, ba tare da tallafin Amirka ba. Gabanin Saudiya ta sanar da hakan, dama can 'yan majalisar dokokin Amirka sun buka ci da Amirka ta kawo karshen wasu bangarorin da ta ke taimaka wa Saudiya musamman a yakin kasar Yemen. A yanzu haka dai Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin jama'a na duniya, suna ci gaba da yin Allah wadai da yakin kasar ta Yamen, inda miliyoyin fararen hula ke cikin bala'i sakamakon yakin na sama da shekaru hudu yanzu.