1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta katse kason kuɗi ga UNESCO

October 31, 2011

Amirka ta yi Allah wadai da amincewa da Paleasɗinu da aka yi a UNESCO, tare da katse kason miliyon 60 na dalar Amirka da ya kamata ta bai wa hukumar kyautata ilimi kimiya da kuma al'adu na duniya.

https://p.dw.com/p/132Ze
cibiyar UNESCO da ke birnin Paris na FaransaHoto: picture-alliance/dpa

Amirka ta nuna rashin jin daɗinta game da bai wa Palesɗinu Kujera da aka yi a hukumar kyautata ilimi kimiya da kuma al'adu na Majalisar Ɗinkin Duniya. Tuni ma dai ƙasar ta Amirka ta aiwatar da barazanar da ta yi tun da farko inda ta katse kason kuɗi miliyon 60 na dala da ya kamata ta zuba wa UNESCO.

Kashi biyu bisa uku na ƙasashen da suka kaɗa ƙuri'a a UNESCO sun amince da Palesɗinu a matsayin cikakkiyar mamba na wannan hukuma, duk kuma da adawa da Isra'ila da kuma uwargijiyarta Amirka ke yi da wannan mataki. Kakakin shugaba Barack Obama wato Jay Carney ya bayyana a fadar mulki ta White House cewa sanya Palesɗinu a cikin wannan hukuma riga malam masallaci da zai iya gurganta yunƙurin sasanta rikicin yankin gabas ta tsakiya.

Ita ma dai Isra'ila ta soki wannan mataki a inda ta ce ba zai haifar wa yankin ɗa mai ido ba. A nata ɓangaren hukumar palesɗinawa ta danganta wannan mataki da nasara na baya-bayannan, a ƙoƙarin da ta ke yi na ganin an amince da ita a matsayin ƙasa 'yantatta. Ƙasashe 14 ne dai suka nuna adawan daga cikin kasshen 173 da suka kaɗa ƙuri'arsu a yayin wata zama da ta gudana a cibiyar hukumar da ke birnin Paris na Faransa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman