1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na neman MDD ta kada kuri'a kan yakin Gaza

June 10, 2024

Sakataren harkokin wajen Amirka, Antony Blinken na ziyara a Masar domin bada gudunmawarsa wajen matsa lamba kan amince wa da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.

https://p.dw.com/p/4gr5X
Amirka na neman MDD ta kada kuri'ar kawo karshen yakin Gaza
Amirka na neman MDD ta kada kuri'ar kawo karshen yakin GazaHoto: Charly Triballeau/AFP/Getty Images

Ana kuma sa ran Amirka ta nemi kwamittin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'a kan daftarin kudurin tsagaita bude wuta nan take, tsakanin bangarorin biyu da kuma sakin mutanen da Hamas  ke ci gaba da garkuwa da su a Gaza.

A ziyarar ta Blinken a wannan makon, zai tattauna da sauran masu shiga tsakani a yakin domin cimma yarjejeniyar tare da tabbatar da cewa, yakin bai yadu zuwa kasar Lebanon ba.

Karin bayani: Blinken na matsa wa Isra'ila lamba don tsagaita wuta a Gaza

Jami'an Amirka dai sun ce, shirin na Isra'ila ne don haka, ta yiwu ta amince da shi, sai dai kuma Kungiyar Hamas ta cacaki Amirka, bayan da ta yi nazari kan daftarin, ta na mai cewa, gwamnatin Washington na kokarin dora alhakin komai kanta.