Muhawara tsakanin Harris da Pence
October 8, 2020Mai shekaru 55 da ke fatan zama macce ta farko mataimakiyar shugaban Amirka idan jam'iyyar Democrat ta yi nasarar zaben na uku ga watan Nuwamba, Kamala Harris ta caccaki abin da ta kira sakacin da gwamnatin Donald Trump ta nuna wajen yaki da annobar corona, wacce ta yi mumunar illa ga kasar. A nasa bangaren dantakarar mukamin shugabanacin kasar karkashin jam'iyyar Shugaba Trump ta Republican, Mike Pence ya zargi Kamala Harris da yaudarar Amirkawa.
Rahotanni dai sun ce an gudanar da muhawarar a cikin tsanaki ba kamar irin wadda Trump da Biden suka yi a baya ba, kana kuma jim kadan bayan kammala muhawarar an samu ra'ayoyi mabanbamta tsakanin 'yan takarar shugabancin kasar a shafukansu na Twitter, inda Trump ya jinjinwa abokin takararsa Pence yayin da shi kuma Biden ya bayyana cewa Harris ta yi gagarumar nasara.