Amirka: Haraji mafi girma kan kayan Turai
October 18, 2019Talla
Amirka ta yi karin kudin fito da kashi 25 cikin dari kan kayayyakin Turai da ake shigarwa cikin kasarta wadanda suka hada da Barasa da Zaitun da Cikwi da sauransu.
Washington ta sanar da daukar matakin ne a matsayin martani dangane da rangwamen da kasashen Turai ke yiwa kamfanin kera jiragen sama na Airbus.
Ta ce tana duba yiwuwar samun dala Biliyan bakwai da miliyan dari biyar daga karin kudin fiton.
Kungiyar ciniki ta duniya WTO wadda ke shiga tsakani kan kasuwanci tsakanin kasa da kasa ta amince da matakin karin harajin.