1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka da Turkiyya sun ce an kashe Khashoggi

Mahmud Yaya Azare MA
October 12, 2018

Jami'an tsaron Turkiyya, sun tabbatar da samun hujjoji da ke tabbatar da cewa dan jaridar Saudiyyar nan Jamal Khashoggi, kashe shi aka yi a cikin ofishin jakadancin Saudiyyar da ke Turkiyya.

https://p.dw.com/p/36S5S
Dschamal Chaschukdschi
Dan jaridar Saudiyya, Jamal Khashoggi, da ya yi batan daboHoto: Getty Images/AFP/M. Al-Shaikh

Kamar yadda tashar talabijin din Aljazeera ta ruwaito, jami’an tsaron na Turkiyya da takwarorinsu na Amirka sun ce dalilan da suka kunshi hoton bidiyo da muryar da aka nada, sun nuna yadda jami'an tsaron Saudiyya 15 da suka iso kasar a ranar Talata 2 ga watan Oktoba, ranar da aka bukaci Khashoggi ya dawo ofishin jakadancin Saudiyyar a Turkiyya domin karbar wasu takardu, sun shiga ofishin jakadancin jim kadan bayan shigar Kashoggin, suka tsare shi suka dinga zaginsa, kafin su lakada masa dukan da har sai da ya sheka lahira, kana suka yi gunduwa-gunduwa da shi da zarto.

Türkei Sicherheitspersonal im Konsulat von Saudi Arabien in Istanbul
Wani jami'in tsaron Saudiyya a TurkiyyaHoto: Getty Images/AFP/B. Kilic

Jami'an Saudiyya wadanda suka isa birnin na Santambul, suka kuma ki ba wa jami’an tsaron Saudiyya izinin shiga ofishin jakadancin, sun ce ba za su iya cewa komai ba dangane da hoton bidiyon har sai an kammala binciken hadin-gwiwa tsakaninsu da Turkiyya.

 

To sai dai kamar yadda Suleimanul Uqaili, wani mai fashin bakin siyasa a Saudiyyar ke cewa, ilahirin wannan batun wata makarkashiya ce ta batanci ko neman rarakar kasar Saudiyyar.

Shugaba Donald Trump na Amirka, da ke fuskantar zazzafar matsin lamba daga sanatocin kasarsa, ya ce a gaskiya ba zai yi garajen babewa da Saudiyya kan wannan batun na Khashoggi ba, yana mai cewa ba zai yadda wannan batun ya jawo masa asarar biliyoyin dalolin da ake samu daga kasuwanci da Saudiyya ba.

Donald Trump und Prinz Mohammed bin Salman
Shugaba Trump da Yerima bin SalmanHoto: picture-alliance/AP Photo/E. Vucci

A hannu guda kuwa, rahotannin da ke fitowa daga kasar ta Saudiyya na nuni da cewa, an tsare wasu ‘ya’yan masarautar da ke guna guni kan abin da ya faru da Kashoggin, wanda ya jima yana hidimta wa masarautar, kafin daga bisani ya koma sukar gyara-kayanka ga Yerima mai jiran gado bin Salman.

 

Masaharhanta dai na hasashen cewa, zai yi wuya burin Yerima bin Salman din ya cika, na darewa kan karagar mulkin Saudiyyar, in har ya tabbata da hanunsa kan zargin kisan dan jaridar, sakamakon kara zezewar tagomashin da yake da shi a ciki da wajen masarautar.