1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka da Koriya ta Kudu za su fara atisaye

Yusuf Bala Nayaya
March 20, 2018

A cewar ma'aikatar tsaron ta Amirka Pentagon wannan atisaye na da manufa ce ta gwaje-gwajen kare kai, ka da ma Koriya ta Arewa ta yi zaton kokari ne na takalarta.

https://p.dw.com/p/2uc55
Südkorea Militärmanöver in Pyeongtaek
Hoto: picture-alliance/dpa/Yonhap/Hong Gi-Won

A ranar daya ga watan Afrilu idan Allah ya kaimu Amirka da Koriya ta Kudu za su koma gudanar da atisayen hadin gwiwa makamancin wanda suka yi a shekarar bara kamar yadda ma'aikatar tsaron Amirka ta bayyana a ranar Litinin. Atisayen na shekarar bana da suka yi wa lakabi da sunan "Foal Eagle" da "Key Resolve," an dakatar da shi ne gudun kada su game a lokaci guda da bikin wasannin Olympic na lokacuin hunturu da aka yi a birnin Pyongchang na Koriya ta Kudu. A cewar ma'aikatar tsaron ta Amirka Pentagon wannan atisaye na da manufa ce ta gwaje-gwajen kare kai ka da ma Koriya ta Arewa ta yi zaton kokari ne na takalarta. Ta kara da cewa an kuma sanar da mahukuntan na Pyongyang kan lokaci da za a yi da ma irin nau'i na atisayen da za a yi.