Amfani da shafukan sada zumunta don yaki da tarzoma
February 27, 2020A yayin taron tattaunawa na mako guda a birnin Legas kan batun sadarwa ta zamani wakilan jihohin Arewa maso gabashin Najeriya da suka halarci zaman taron sun bayyana yadda suke samun ci-gaba ta wannan siga duk kuwa da kalubale da ke tattare da tsarin a Najeriya.
Najeriya dai ta fada cikin wani irin wadi na tsaka mai wuya musamman ta fannin tsaro inda yawancin 'yan kasar ke zaman dar-dar. To amma batun sadarwar zamani ta "Social Media" na tallafawa mazauna yankin Arewa maso gabashin Najeriya.
Bulama Yarima dan jarida ne kuma kwararre daga jihar Borno ta fannin sadarwar zamani ya yi kari haske kan gudummowar tsarin ta fannin tsaro.
"Muna amfani da hanyoyi da dama don bayar da gudummowa ta fannin tsaro da kasuwanci a jihar Borno ga misali akwai CJTF akwai Borno Frontiers akwai Elders Forum kuma duk muna musayar ra'ayi a dangane da halin da ake ciki ta tsaro da kasuwanci."
A jihar Adamawa ma ana cikin fargaba ta kai farmaki tare da haifar da tsaiko ta fannin kasuwanci, saboda haka ne ma Malam Shuaib Maidala, kwararre ta fannin "Social Media" ya ce:
"Batu na kasuwanci da tsaro a jihar Adamawa muna kokari muna fadakar da jama'a su san halin da ake ciki musamman idan an kai farmaki ko kuma alamun haka, ana fadakar da mutane kuma ana ci gaba da gudanar da kasuwanci ta "online" sosai."
A yankin baki daya dai hukumomi da kungiyoyi sun tashi haikan don gyare-gyare ga inda tashin hankali ya daidaita, inda Malam Shatima Iliyas wanda ya fito daga jihar Yobe ya ce sun daura damarar yaki na inganta rayuwar jama'a tare da fadakarwa ta "Social Media".