1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Ambaliyar ruwa ta yi barna

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 16, 2020

Mamakon ruwan sama da iska mai karfi da suka haddasa ambaliyar ruwa a Sudan, sun yi sanadiyyar asarar rayuka sama da 60 tun cikin watan Yulin da ya gabata kawo yanzu, tare kuma da tilastawa dubban mutane barin gidajensu.

https://p.dw.com/p/3h2nB
Sudan Überschwemmungen
Hoto: Reuters/A. Campeanu

Cikin wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin cikin gida ta Sudan din dangane da kiyasin da wata kungiya mai zaman kanta ta fitar, ta bayyana cewa sama da gidaje dubu 14 da gine-ginen ma'aikatu da hukumomin gwamnati 119 sun rushe, yayin da wasu gidajen sama da 16 suka lalace. Ofishin Hukumar Kula da Bayar da Agajin Gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya, ya nunar da cewa sama da mutane dubu 185 ne bala'in ambaliyar ruwan ya shafa. Dama dai Sudan na fama da irin wannan ibtila'i na ambaliya a duk shekara, tsakanin watan Yuli zuwa Oktoba.