1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliyar laka ta kashe mutane 17 a Brazil

Gazali Abdou tasawaNovember 6, 2015

Lamarin ya wakana ne bayan da wata madatsar ruwa da ke tare dagwalon kamfanin Samaco mai aikin hakar arzikin ma'adanai a kauyen Bento Rodrigues na Brazil ta karye.

https://p.dw.com/p/1H0uk
BdT Grubenunglück in China
Hoto: AP

A Brazil mutane 17 sun halaka a jiya Alhamis a kauyen Bento Rodrigues na Kudu maso Gabashin kasar a cikin wata ambaliyar gurbatacciyar laka da ta biyo bayan faduwar wata madatsar ruwan dagwalon kamfanin Samaco mai aikin hakar zinari da karafa.

Shugaban hukumar 'yan kwana-kwana ta birnin Marina Adao Severino ya ce ko baya ga mutanen da suka mutu wasu sama da 50 sun ji rauni kuma wasu mutanen sama da 40 sun bata babu labarinsu.

Gidan Talabijin na Globo na kasar ta Brazil ya nuno irin yanda gurbatacciyar lakar ta mamaye motoci dama gine-ginen kauyen . Ana ci gaba da ayyukan ceto ga al'ummar kauyen na Bento Rodrigues mai kunshe da mutane 600