Kaduna: Ta'addanci ya hada kan al'umma
July 13, 2022Rigin-gimun kabilanci da addini tare na da siyasa, sun dade suna janyo asarar rayuka da dukiya mai tarin yawa tun sama da shekaru 30 da suka gabata a yankin kudancin kaduna. Wannan matsala dai, na haddasa zaman gaba da juna da ramuwar gayya da kisan dauki dai-dai a kan hanya. To sai dai a yanzu rashin tsaro da hare-haren ta'addanci da ma ayyukan masu sata da garkuwa da mutane, ya sanya dukkanin kabilun yankin hada kansu domin daukar matakan magance munanan ayyukan maharan da ke farwa mazauna wadannan yankuna.
Karin Bayani: Rashin tabbas ga rayuwar al'ummar Najeriya
Alhaji Hassan Abdullahi Wamban jama'a shi ne shugaban Gidauniyar Jama'a da kuma ya kasance babban basarake a kudancin Kadunan, ya nunar da cewa lokaci ya yi da dukkanin alummar yankin za su gane cewa akwai bukatar hada kai da duk wanda ke son zaman lafiya domin kawo ci-gaba a yankin ta dukkanin hanyoyin da suka jibanci kasa da al'umma baki daya. Rahotannin sun nunar da yadda hare-haren ta'addancin da 'yan bindigar ke kai wa a yankin, ya tursasa dubban mutane yin gudun hijira yayin da wasu da dama suka rasa matsugunnansu.
Dakta Auwal Aliyu Abdullahi wani kwararren masanin tsaro ne a Najeriya da ke cewa dole kanwar naki ta sanya al'ummar kudancin Kadunan hada kai a wannan lokacin, domin ba su da wani zabi da ya wuce hakan. Ya kuma kara janyo hankalin hukumomi a kan kara ribanya kokari wajen samar da zaman lafiya a daukacin yankin, domin magance rashin ci-gaba da ke addabar daukacin alu'mmarsa. Ya ce ya kamata al'umma ta rinka bayar da tata gudunmawar, wajen samar da kyakkyawan yanayi da zai bunkasa zamantakewa da kawo karshen rigin-gimun siyasa da na bangaranci.
Karin Bayani: Shawo kan matsalar tsaro a Najeriya
Shi ma da yake bayar da nasa tsokacin, shugaban kungiyar Miyatti Allah reshen jihar Kaduna Mallam Haruna Tujja cewa ya yi, ya kamata gwamnatin Najeriya ta zauna da dukkanin bangarorin masu tawaye domin samun zaman lafiyar kasa. A nasu bangaren kwararru a bangaren tsaro da zamantakewa, sun nuna fargabarsu ga makomar mallakar makaman kare kai da alummar gari ke yi a matsayin wani abun tsoro nan gaba.