Al'ummar Gambiya na zaben 'yan majalisa
April 6, 2017Talla
Al'ummar Gambiya na zaben 'yan majalisar dokoki a karon farko tun bayan karshen gwamnatin Shugaba Yahya Jammeh, zaben da ake ganin zai bada dama ga 'yan takarar jam'iyyu su shiga a dama da su a majalisar, sabanin tsawon shekaru 22 da aka gani kusan jam'iyya guda mai mulki ke kida ta yi awarta a majalisa.
Akwai dai jam'iyyu tara da suke fafatawa da juna a zaben na wannan rana ta Alhamis ciki kuwa har da jam'iyyar APRC ta Jammeh da jam'iyyar UDP. 'Yan Gambiya 880,000 suka cancanci kada kuri'a a zaben da za a fara takwas na safe har i zuwa biyar na yamma. Akwai dai kujeru 53 na 'yan majalisar da jam'iyyu za su nema baya ga biyar da ke zama nadi daga bangaren shugaban kasa.