1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Aski ya zo gaban goshi

Isaac Kaledzi MAB
December 6, 2024

Fiye da 'yan Ghana miliyan 18 ne ake sa ran za su kada kuri'unsu a zaben gama gari da zai gudana ranar Asabar 7 ga watan Disamban 2024.

https://p.dw.com/p/4nqwd
 John Dramani Mahama da Mahamudu Bawumia
John Dramani Mahama da Mahamudu BawumiaHoto: Nipah Dennis/AFP/Getty Images, Olympia de Maismont/AFP

'Yan takara  goma sha daya ne ke zawarjin kujarar shugabancin kasar Ghana. Amma fafatawar neman wannan babban mukami ya fi zafi tsakanin mataimakin shugaban kasa Mahamadu Bawumia daga jam'iyyar NPP mai mulki da kuma John Dramani Mahama na jam'iyyar NDC, wanda ya rike mukamin shugaban kasar Ghana tsakanin shekarar 2013-2016. Hasali ma dai, Mahama ya tsaya takara a karo na uku ke nan, bayan rashin nasara a hannun shugaba mai barin gado Nana Akufo-Addo, wanda ya yi wa'adi biyu. Sai dai Bawumia da ke zama mataimakin Akufo-Addo, na fatan tsawaita mulkin wa jam'iyyarsu a zaben bana. Hukumar zaben Ghana ta fuskanci zargin rashin adalci daga wasu jam'iyyun siyasa. Matakin da ta dauka na takaita sa ido kan kafafen yada labarai a lokacin tattara sakamakon zaben ya haifar da   cece-kucea kasar, lamarin da ya sa ta lashe amanta. Ko da shugaban hukumar ta zabe Jean Mensa, sai da ya yi alkawarin gudanar da sahihin zabe kuma cikin lumana: "A madadin hukumar zabe ta Ghana, na yi alkawarin cewa ni da tawaga ta za mu ci gaba da gudanar da ayyuka da zu tabbatar da zaman lafiya kafin a yi zabe da ranar zabe da kuma bayan zaben 2024. Hanyoyin da za mu yi amfani da su a ranar zabe da kuma a cikin kwanakin da za su bi baya zabe za su kasance masu karfi da nagarta da rashin nuna bambanci. Sakamakon da za mu ayyana zai nuna ra'ayin 'yan kasar kamar yadda suka bayyana a rumfunan zabe." Baya ma ga zaben shugaban kasar Ghana, masu kada kuri'a za su yi zaben 'yan majalisa sama da 270 a runfuna sama da dubu 40,000 da ke fadin kasa. 'Yan Ghana na da matsaloli da dama da suke son dan takarar da ya yi nasarar lashe zaben shugaban kasa ya magance musu, ko ma daga wata jam'iyya ya fito. Amma gwiwarsu ta karaya saboda sau da yawa ba sa cika alkawuran da suka yi yakin neman zabe.

Ghana Vorwahl John Dramani Mahama
Hoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Sai manyan 'yan takara biyu wato  Bawumiada Mahama sun mayar da hankalinsu kan hanyoyin da za su bi wajen farfado da tattalin arzikin Ghana, wanda ya kasance kalubale a gwamnatin Akufo-Addo mai barin gado. A halin yanzu dai, Ghana na karkashin shirin Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF don neman farfado da komadar arziki. Hasali dai, sakamakon karbo rancen da ta yi na tsawon shekaru, fadar mulki ta Accra ta gaza biyan mafi yawan basussukan da ake bin ta, wanda ya kai dala biliyan 30. Amma Bawumia na NPP da ke zama masanin tattalin arziki kuma tsohon ma'aikacin babban bankin Ghana, ya yi alkawarin dogaro kan hanyar zamani ta dijital wajen magance matsalolin tattalin arzikin  Ghana: "Dalilin da ya sa muke neman mulki shi ne mu yi amfani da shi wajen samar da ci gaba ga al’ummar kasar nan. Don haka na yi alkawarin yin aiki bisa mutunta ka’ida da kuma hada kai da kowa don ganin an yi zabe cikin kwanciyar hankali."

Ghana | Wahlen - Unterstützer von NPP Kandidat Mahamudu Bawumia
Hoto: NIPAH DENNIS/AFP

Shi ma John Mahama na NDC da ke kalubalantar dan takarar gwamnati, ya yi ta yayata manufofin tattalin arziki na jam'iyyarsa, wanda ya ce za su sakar wa tattalin arzikin Ghana mara tare da samar da zaman lafiya mai dorewa: " Na zo nan a yau ne ne domin in bayyana manufofin kaina da na jam’iyyata National Democratic Congress, na ganin an samar da wannan zaman lafiya. Da farko, muna tabbatar da cewa mu a NDC, muna ci gaba da tsayawa tsayin daka don gina kasa mai zaman lafiya da wadata tare kuma da cika burin duk al'umarmu." An saba gudanar da zabe a Ghana cikin kwanciyar hankali kuma masu sa ido ba sa tsammanin za a samu sauyi a wannan karon ma. Tuni dai 'yan takara da ke zawarcin shugabancin kasa sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, inda suka yi alkawarin amincewa da sakamakon  zaben.