Bala'in wutar daji ya mamaye Aljeriya
August 11, 2021Kasashe da dama da ke gabar Tekun Bahar Rum dai na fama da bala'in wutar dajin, kuma Aljeriyan na daga cikin kasashen da bala'in ya fi shafa. Rahotanni sun nunar da cewa, cikin mutanen da suka rasa rayukansu a ibtila'in wutar dajin, 28 sojoji ne da gwamnati ta tura gundumar Kabylie mai cike da tsaunuka domin taimakawa wajen kawo karshen wutar dajin da ke ci gaba da ruruwa. Tuni dai shugaban kasar Abdelmadjid Tebboune ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki, tare kuma da dakatar da duk wasu ayyuka da ba su shafi wutar dajin ba. Kimanin wutar dajin 100 ke ci ganga-ganga musamman a yankunan Tizi Ouzou da Bejaia. Kasashen Turkiyya da Italiya da kuma Girka, na daga cikin kasashen da ke jin jiki a bala'in na wutar daji da ke ci gaba da lakume dukiyoyi har ma da rayukan al'umma.