Bouteflika ya amince ya sauka daga mulki
April 1, 2019Talla
Tun a ranar Asabar da ta gabata ne, shugaban hafsan sojojin kasar ya ja hankalin fadar gwamnati mai mulki, da ta aiwatar da ayar dokar, wacce za ta kai ga nada shugaban majalisar dokokin a matsayin shugaban rikon kwarya na kasar, matakin da ke zuwa jim kadan baya da Shugaba Bouteflika, ya sanar da nada sabin ministoci.
Ana ganin ajiye mulki da shugaban ke shirin yi, zai iya kawo karshen dambarwar siyasar da kasar ta fada bayan da al'ummarta suka kwashi makonnin suna zanga-zangar adawa da mulkin Bouteflika na kusan shekaru ashirin.