1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aikin hajji na karshe a jerin ayyuka

Abdourahamane Hassane
July 31, 2020

Alhazai da ke gudanar da aikin hajjin bana sun shiga ranar ta karshe ta aikin ibadar  na jifar shedan daya daga cikin gishikai na aikin  hajin bayan kammala tsayuwar Arafat.

https://p.dw.com/p/3gEkw
Saudi-Arabien Hadsch in Mekka
Hoto: Reuters/Z. Bensemra

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan Sallah Layya a fadin duniya koi'na a cikin kasashen Musulmi. A bana an takaita yawan mahajjatan saboda annobar corona wanda dukka-dukka gomai na miliyoyin mutane mazauna Sauduiyar kadai aka bai wa izinin yin hajjin, sabanin shekarun baya inda Muslmi kimanin miliyan biyu da rabi ke gudanar da aikin hajjin.