1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alhazzai sun isa dutsin Arafa

Abdoulaye Mamane Amadou
July 8, 2022

An shiga matakin kololuwa na aikin hajjin bana a wannan rana, inda mahajjata daga sassan duniya suka isa dutsin Arafa don ci gaba da gudanar da ibada.

https://p.dw.com/p/4Dq8C
Saudi-Arabien | Mekka Hadsch
Hoto: Ashraf Amra/AA/picture alliance

A wannan Jumma'ar alhazzai ke fita filin Arfa a ci gaba da aikin hajjin wannan shekara da maniyata fiye da miliyan daya da rabi daga sassa dabam-daban na duniya ke gudanarwa.

Bayan shafe daren jiya da aka soma shiga kololuwar aikin na hajjin bana a Mina, maniyatan za su shafe tsawon wunin yau suna ibada a dutsin Arafa, kafin kwana a Muzdalifa, wanda hakan ke daga cikin muhimman ranakun aikin hajjin.

Wannan ne dai karon farko da ake aikin hajjin cikin shekaru uku tun bayan bullar annobar Corona a fadin duniya. Aikin hajjin dai na daga cikin shika-shikan Musluncin da ya wajaba a kan kowane Musulmin da yake da gwargwadon hali na sauke faralin.