Alhaji Bamanga Tukur ya zama shugaban PDP
March 23, 2012A Tarayyar Najeriya an zabi tsohon gwamnan jahar Gongola Alhaji Bamanga Tukur a matsayin sabon shugaban jam'iyyar PDP. Kamfanin dillalcin labaran Najeriya ya ruwaito cewa wakilai fiye da 4500 da suka hallara a dandalin taro na Eagle Square dake Abuja sun zaɓi Alhaji sun tattabar ta zaben Alhaji Bamanga Tunkur, wanda dama can shine zaɓin shugaban ƙasar Goodluck Jonathan, sabanin yadda kwamitin zaɓen ya tantance sauran yan takara a jiya, a yau sauran yan takara suka janye kuma aka bi zaɓin shugaba Jonatahan. An kuma tabbatarwa tsohon gwamnan jihar Osun Olagunsoye Oyinlola muƙamin sabon sakataren jam'iyyar ta PDP na ƙasa. Su dai sauran yan takaran da suka janye sunce bo dole aka sa su ba, amma sun yi haka ne wai don ci gaban jam'iyyar.
Gabanin zaben dai jam'iyyar PDP ta shiga rudani. Wannan lamarin ya shafi ɓaraka a jam'iyyar ta PDP ya sanya zababbun gwamnonin PDP na jihohin arewa suka fara juya wa shugaban kasa da ke kokarin tursasa masu Alhaji Bamanga Tukur dan ya lashe zaben shugabancin jamiyyar.
A yanzu haka dai zaben shugaban jamiyyar PDP na kasa na ci-gaba da fuskantar koke-koke da suka daga bangarori daban daban na jiga-jigai da 'ya'yan jamiyyar ta PDP, adangane da tsawayar takaran Alhaji Bamanga Tukur mai shekaru 80 haifuwa da za a fafata da shi a dandalin taro na na Eagle Square dake a babban birnin Tarayya Abuja.
Tuni dai jiga-jigan PDP wadanda suka kafa jamiyyar a Najeriya da wasu manyan 'yan siyasar kasar suka fito karara cewa sun gaji da ganin yadda dattawa ke jagorantar jamiyyar ta PDP, tun akalla shekaru 13 kenan da dawowar mulkin farar hula a Najeriyan. Acewar su lokaci ya yi na sabbin jini dan kawo sauyi ga ci-gaban alumma da kuma fidda su daga cikin kangin talauci da tashe-tashen hankula da suka fada, da zummar samun dauwamanmiyar mulkin demokuradiyya, ba tare da danne hakkin wani talaka ba, kamar dai yadda Alhaji Umar Gana daya daga chikin wadanda suka kafa jamiyyar PDP a Najeriya ya bayyana a wajan taran yan jaridu a kaduna
"Akwai bukatar dakatar da dattijai a dukkanin zabubbukan dake gabatowa a Najeriya, saboda irin rawar da suke takawa na haifar da matsaloli a cikin kasar, da kuma yadda suke toshe dukkanin hanyoyin da suka wajaba na tabbatar da ganin cewa sun kashe kwarin gwiwar matasa daga fitowa a matsayin yan takara, Alhaji Bamanga Tukur ya dade ana damawa da shi a harkokin siyasa Najeriya, saboda haka ya kamata ya koma gida, ya sake lale, maimakon fitowa a matsayin dan takara, ya kamata ya sanya karamin yaro ya fito a dama da shi maimakon shi kansa"
Rahotannin sun nunar da cewa hatta jamiyyun adawa da gwamnoni a Najeriya ba su gamsu da yadda shugaban kasa ke yunkurin marawa Bamanga Tukur baya ba, inda suke ganin cewa za ayi amfani da shine wajan yin murdiya tare da yin tazarce a shekara ta 2015, wannan ya sanya gwamnoni da kungiyoyin dake fafatukar ci-gaban mulkin demokuradiyya a Najeriya suka tashi tsaye wajan ganin wadanda za su yi zabe da su tabbatar da ganin cewa sun turje, kuma sun duba wadanda suka cancanta don baiwa matasa damar fitowa a dama da su, ta yadda a magance matsalolin da arewa ta fada na rashin ci-gaban alumma sakamakon yadda dattawan yankin suka yi kane -kane a kan madafun iko, suka kuma ki bayar da damaga matasa a harkokin siyasa inji Alhaji Umar Gana shugaban kamfe na shugaban Goodluck Jonathan a yankin jihojin arewa
"A kowane lokaci sai su rika fakewa da sunan Sardauna suna cutar da alu'mman yankin, lokaci ya yi da dukkanin masu kishin ci-gaban mulkin siyasa a Najeriya, za su fito su shiga cikin yakin da muke yi na kakkaɓe dattawan dake hana ruwa gudu a cikin wannan kasa, domin an yi da su a shekarun baya, anyi da su a yau, kuma suna aci gaba da yi da su har a abada, lallace wadannan dattawa su koma gida su huta sabo da zamanin su ya wuce, akwai sabbin jini masu fasaha da bajinta ta dukkanin hanyoyin da suka cancanta na ci-gaban kasa da alumma baki daya"
Alhaji Samaila mai Atampa wani babban jigo a jamiyyar PDP a jihar Kaduna yace ya kamata duk wanda ya san cewa ya sha kaye tun daga yankin sa, to fa ya san cewa, akwai babban kalubale a gaban sa wajan tunkarar babban zabe, tunda dai yar none ta riga ta nuna, wanda ya fadi sai ya dauki kaddara.
Tun a ranar Alhamis ne dai kafafen watsa labarai na cikin gida dana kasashen ketare ke ta ruwaito irin martanin da Alhaji Bamanga Tukur ke maidawa, inda yake cewa kujerar shugabancin jamiyyar PDP ba ta kananan yara bane, saboda haka sabbin jini su kauce, kuma yana da 'yancin fitowa a fafata da shi a matsayin sa na dan kasa acewar sa dukkannin zabubbukan da aka gudanar a wasu jihohin arewa, ba zabe ba ne aka yi, illa murdiya zalla da kuma danne masa hakkin sa da kundin tsarin mulki ya bashi
Mawallafi: Ibrahima Yakubu
Edita: Usman Shehu Usman