SiyasaTarayyar Rasha
Alexei Navalny zai shiga matsi
September 27, 2023Talla
Navalny yace daga wannan kin sauya hukuncin da kotun daukaka kara ta yi, to tabbas hukumomi za su yi aiki da umarnin kotu, wace ta yanke hukuncin a tura shi ga gidan yari mafi tsauri kuma na musamman a kasar. Dan shekaru 47 a duniya Alexei Navalny wanda kamanninsa suka yi matukar sauyawa a 'yan watanni da yake daure, ya wallafa a shafinsa cewa tun bayan da kotu ta yanke hukunci to dole zan kasance cikin gidan yari na musamman tsawon watanni 12 dake tafe.