Hare-haren Saudiya na jefa fararen hula cikin tasku
April 18, 2015Majalisar Dinkin Duniya ta ce daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu a wannan yaki da Saudiya ke jagoranta yayin da dubun-dubatar iyalai suka kauracewa matsugunansu inda kuma sojojin Saudiyan shida suka rasa rayukansu. Majalisar ta kara da cewa ana bukatar kudi da yawansu ya kai dalar Amirka miliyan 274 domin bada agajin gaggawa ga al'ummar Yemen din da yaki ya rutsa da su. Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa tuni kasar Saudiya ta sha alwashin bayar da baki dayan wadannan makudan kudaden.Tsahon makawanni uku ke nan dai kasar ta Saudiya ke jagorantar kawayenta suna yin barin wuta a kasar ta Yemen musamman a yankunan da 'yan tawayen na Huthi da ke zaman Musulmi mabiya Shi'a suke rike da madafun iko, hare-haren kuma da ke ci gaba da lakume rayukan fararen hular kasar.