Alamar samun masalaha a yankin Koriya
January 2, 2018
Tun a jawabin sabuwar shekara shugaban kasar Koriya ta Arewa, ya nuna yunkurin yin amfani da kakar wasannin Olympics mai zuwa da za a gudanar a kasar Koriya ta Kudu don daidaita dangantaka tsakanin kasashen.
Bayan shekara guda da ya kwashe yana barazanar makaman kare dangi, a halin yanzu shugaba Kim Jong Un na kasar Koriya ta Arewa ya yi amfani da sakon sa na 2018 dayin kira da a samu kyakykyawar alaka a yankin Koriya, ya kuma kara da jaddada kudirin kasar na bada gudunmawa wajen gudanar da wasannin masu zuwa.
A nata bangaren kasar Koriya ta Kudu dama ta dade tana neman wannan dama daga makobciyar ta ta Koriya ta Arewa, don ganin ba a kassara kasar wasannin ba da wani gwajin na makami mai linzami, don haka shugaban kasarsu ya yi saurin yin maraba da tayin sulhu da Koriya ta Arewa.