Hadaddiyar Daular Larabawa ta kulla alaka da Isra'la
August 14, 2020Ana dai ganin wannan alaka, ba ta rasa nasaba da batun samun huldar kasuwanci tsakanin hadaddiyar Daular Larabawan da Isra'ila. Wannan yarjejeniya dai na zuwa ne, adaidai lokacin da Isra'ilan ke ci gaba da daukar matakan da ke wa kallon na hana samuwar kasar Falasdinu. Da yake tsokaci kan batun, shugaban Amirka Donald Trump ya bayyana cewa an cimma yarjejeniya Haddiyar Daular Larabawan da ya ayyana da babbar abokiyarsa a yankin Gulf da kuma kawar Amirka ta har abada wato Isra'ila, yana mai cewa yarjejeniyar ita ce matashiyar ci gaba da zaman lafiya a yankin.
An dai yi wa wannan yarjejeniya lakabi da "Abraham Agreement," yarjejeniyar kuma da shugaban Amirka Donald Trump da ya kai gwauro ya kai mari a kanta, inda ya ce a karkashinta Isra'ila ta aminta da dakatar da yunkurin da take yi na mamaye wani yanki na Gabar Yamma da Kogin Jordan. Koda yake a jawabin da firaministan Isra'ilan Benjamin Natenyahu ya yi wa 'yan kasarsa, ya ce jinkirta mamayar za a yi ba wai dakatar da ita gaba daya ba.
Hadaddiyar Daular Larabawan dai na zaman kasar Larabawa ta uku da ta cimma irin wannan yarjejeniyar da Isra'ila bayan Jordan da Masar, kuma ministan harkokin wajenta Anwar Qirqash ya ce yarjejeniyar ita ce kyakkywan azanci. Tuni dai hukumar Falasdinawa wacca ta janye jakadanta da ke kasar ta Haddiyar Daular Larabawan, ta bakin kakakinta Nabeel Abu Rudainah ta siffanta yarjejeniyar da babbar cin amanar al'ummar Falalsdinu.
Kungiyar Hamas mai gwagwarmaya da makamai kuwa, cewa ta yi da ma tasan za a rina wai an sace zanin mahaukaciya. Jordan ta ce yarjejeniyar na iya zama tubalin ci gaba da tattaunawar sulhu, idan har ta yi nasarar jan hankalin Isra'ila ta amince da samar da kasar Falasdinu a yankin da ta mamaye lokacin yakin kasashen Larabawa da Isra'ila a shekarar 1967. Shi kuwa shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi abokin Hadaddiyar Daular Larabawan, lale maraba ya yi da yarjejeniyar da ya siffanta da aikin jarimai.