1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Eyimba ta Najeriya ta fara farfadowa a Confederation Cup

Mouhamadou Awal Balarabe SB
January 6, 2025

Manchester United ta jajirce wa Liverpool a kare ji biri jini da suka yi a Premier Legue, yayin da PSG ta lashe kofin gwani na gwanayen Faransa bayan doke Monaco a birnin Doha.

https://p.dw.com/p/4oroD
Wasan Pirimiya ta Ingila: Manchester United da FC Liverpool
Wasan Pirimiya ta IngilaHoto: Dave Thompson/AP/picture alliance

Amurka ta lashe kofi united na tennis a karo na biyu a tarihinta a daidai lokacin da Chaina ke neman hanyoyin ci gaba da tasiri a fagen tennis da ake bugawa a kan teburi.

Za mu yaye kallabin shirin ne da Afirka, inda aka gudanar da wasannin mako na hudu na gasar kwallon kafa ta neman cin kofin zakarun wannan nahiya. Abin da ya fi daukar hankali shi ne yadda TP Mazembe ta Jamhuriyar Dimnukaradiyyar Kwango ta sake yin abin fallasa inda ta sha duka tamkar kurar roko da ci 0-3 a hannun Young African ta Tanzaniya, lamarin da ya sa kungiyar ta Lubumbashi zama 'yar baya ga dangi da maki uku a rukunin farko. A daya hannun kuwa, Al Hilal ta Sudan ta dare saman rukuni a maki goma, bayan da ta jajirce wa MS Alger har ta farke kwallon da ake binta kuma aka katshi 1-1. A rukuni na biyu kuwa, AS FAR ta Maroko ce ke kan gaba sakamkon doke Maniema Union ta Kwango da ci 2-0, yayin da Raja Casablanca ta Maroko samu nasara a kan Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu da ci daya mai ban haushi, lamarin da ya bai wa wakiliyar kasar Nelson Mandela zama ta biyu a wannan rukuni.

Karin Bayani: Ghana ta yi kunnen doki da Najeriya a share fagen shiga CHAN

Wasan zakarun Afirka | ES Tunis da Al Ahly (2023)
Wasan zakarun AfirkaHoto: Ahmed Gomaa/Xinhua/picture alliance

Sai dai a rukuni na uku, al-Ahly da ke rike da kofin zakarun kwallon kafa na nahiyar Afirka ba ta ji dadi ba, domin Belouizdad ta lallasa ta da ci 1-0. A wannan marra dai, Misirawan sun rasa matsayinsu na ja gaban rukuni, inda maimakon haka Orlando Pirates ta Afirka ta Kudu ta koma matsayin farko bayan da ta mamaye Stade Abidjan ta Cote d Ivoire da 3-0. A rukuni na hudu kuwa na karshe kuwa, Esperance ta Tunisiya ta fadi kasa warwas da ci 1-2 a hannun Pyramid FC ta Masar, amma kungiyar birnin Tunis na ci gaba da rike saman teburi. Ita kuwa Sagrada Esperanza ta Angola ta doke Dliba ta Mali da ci 1-0.

A confedeation cup kuwa, Enyimba da ke wakiltar tarayyar Najeriya ce ta fi taka rawar gani, inda ta mamaye Black Bulls ta Mozambik da 4-1a wasan mako na hudu. Sai dai tana ci gaba da zama 'yar baya ga dangi a rukuninta na biyar, wanda Zamalek ta Masar take ci gaba da mamaye bayan canjaras 0-0 da ta yi da 'yar uwarta ta Masar wato Al Masry. 

Wasan zakarun Afirka | Viertelfinale, Maroko da Algerien
Wasan zakarun AfirkaHoto: Shaun Roy/Sports/empics/picture alliance

Ita kuwa Constantine ta Aljeriya da ke jan raganar rukunin farko ta gasa wa Bravos do Maquis ta Angola aya a hannu da ci 4-0, yayin da Simba ta Tanzaniya da ke a matsayi na biyu ta bi CS Sfaxien ta Tuniya har gida kuma ta doke ta da ci 1- 0-1. A rukuni na biyu kuwa, Berkane ta Maroko ta bi Stade Malien ta Mali har gida kuma ta doke ta da 1-0. Haka ita ma Stellenbosch ta Afrika ta Kudu ta lallasa CD Lunda Sul ta Angola da ci 2-0.  A rukuni na hudu kuwa,  ASEC Mimosas ta Cote d' Ivoire da  USM Alger sun yi kunnen doki 1-1. Ita kuwa Jaraaf ta Sen ta ci kwallo daya 1-0 a gaban Orapa United ta Botswana.

Yanzu kuma sai nanTurai, inda bayan hutun kirsimeti da na shiga sabuwar shekara, manyan lig da dama sun koma fagen wasanni, in ban da Bundesliga ta Jamus da ke fara wasa a cikin wannan mako. A gasar Premier League ta Ingila, gwajin kwanji tsakanin Manchester United da Liverpool ne ya fi daukar hankali, ko da yake an tashi babu kare bin da damo wato 2-2 tsakanin abokan hamayyar guda biyu. Amma dai tauraron Liverpool Mohamed Salah dan asalin Masar ya sake zura kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida, wanda ya kai jimillar kwallayensa zuwa 18 tun farkon kakar wasa ta bana. Kuma Reds na ci gaba da zama a saman teburin Premier, inda ta zarta Arsenal da ke a matsayi na biyu da maki shida. A nata bangaren, Manchester City ta samu nasara ta biyu a jere bayan da ta doke West Ham da ci 4-1.

Wasannin Turai | Olympiacos FC da ACF Fiorentina
Wasannin TuraiHoto: Aris Messinis/AFP/Getty Images

A Italiya kuwa, Napoli ta ci gaba da zama a kan gaba bayan nasarar da ta samu a kan Fiorentina da ci 3-0, amma Atalanta Bergamo ta Ademola Lookman da ke a matsayi na biyu na cin dunduniyarta. Su kuwa Inter da AC Milan suna da wasa daya da ya rage, saboda a halin yanzu kungiyoyin biyu na kasar Saudiyya inda za su buga wasan Super Cup na Italiya a yammacin wannan Litini.

A gasar Ligue 1 ta Faransa, Marseille ta fara wannan shekara da kafara dama inda ta doke Le Havre da ci 5-1. Duk da cewa ita ce ta 2 a kan teburi, amma ba ta kusanci kafadar PSG ba, wacce jiya Lahadi a birnin Doha ta buba wasan neman cin kofin gwani na gwanayen kwallon kafar Faransa da Monaco, kuma ta samu nasara da ci 1-0 sakamakon kwallon da Ousmane Dembélé ya zura a minti karshen wasa, lamarin da ya faranta wa Luis Enrique, kocin na Paris Saint Germain rai.

Wasannin Turai - PSG da FC Barcelona
Wasannin TuraiHoto: Mohammed Badra/EPA

Wannan dai shi ne karo na 13 da PSG ke lashe wannan kofi da ke gudana tsakanin kungiyar da ke rike da kambun zakara da wacce ta lashe kofin kwallon kafar kasar.

A Spain, labarin ya tabbata bayan makonni na kwan-gaba kwan-baya, Dani Olmo da matashin Pau Victor ba za su iya buga wa FC Barcelona wasa a zango na biyu na kakar wasa ba. Wannan ya zama babban naushi ga kungiyar ta Spain wacce ta biya miliyan 60 don sayan Olmo da ke zama tsohon dan wasan RB Leipzig ta Jamus.

A fagen tennis, kasar Amurka karkashin jagorancin Coco Gauff da Taylor Fritz ta lashe kofin United  karo na biyu cikin shekaru uku, bayan da ta doke Poland da ci 2-0 a ranar Lahadi a wasan karshe a birnin Sydney. Dama dai Amurka ta nuna burinta na samun nasara a wannan gasa mai gauraya rukunonin 'yan tennis, wacce WTA da ATP suke hada gwiwa wajen shiryawa tun 2023.

Coco Gauffs
Coco GauffsHoto: Charles Krupa/AP/picture alliance

Ita dai Coco Gauff, mai matsyi na uku a duniya ce ta fara nuna hanya ta hanyar mamaye Iga Swiatek mai matsayi na biyu da rukunin ci 6-4, 6-4, yayin daga bisani Taylor Fritz mai matsayi na hudu a duniya ya samu nasara a kan Hubert Hurkacz mai matzayi na 16 da rukunin ci 6-4, 5-7, 7-6 (7/4). Wannan dai shi ne karo na biyu a jee da Poland ta kasa samun nasara a gasar Uniter cup baya ga wacce ta gudana a Jamus a bara.

Idan muka leka fagen kwallon Tenis da ake bugawa a kan teburi kuwa, babakeren da kasar China ta yi wa wannan wasa na tsawon shekaru na fuskantar babban kalubale, sakamakon yunkurowar da matasan 'yan wasan Turai suka yi, musamman ma na nan Jamus don kawar da ita, inda suka dauki gabaren bunkasa fannin wasan don kara samun karbuwa.

Dan kasar Japan Hideki Matsuyama ya lashe gasar golf ta Sentry a Hawai na Amurka a ranar Lahadi, tare da kafa sabon tarihi na samun ramuka 72 a gasar da ke zama ta farko ta kakar wasa ta bana. Wannan dai ita ce nasara ta 11 da Matsuyama mai shekaru 32 ya samu a tarihinsa na golf, inda ya zarta Ba'amurke Collin Morikawa da bugu uku. Sannan Matsuyama da ya lashe lambar tagulla a gasar Paris, ya nuna kwarewa a duk zagaye hudu da ya yi, lamarin da ya ba shi damar doke tarihin da Cameron Smith dan kasar Ostareliya ke rike da shi tun shekarar 2022. Wanda ya samu matsayi na uku a wannan gasa ta golf, shi ne  Im Sung-jae da ya fito daga Koriya ta Kudu. Gasa ta gaba ta golf za ta gudana a ne a arshen wata a Pebble Beach da ke California.