1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Samun nasara kan kungiyoyin 'yan bindiga a Afirka ta Tsakiya

Abdourahamane Hassane MNA
February 17, 2020

Gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta yi nasara kakkabe kungiyoyin mayaka a sassa da dama na kasar wanda da farko kusan kashi uku bisa hudu na kasar ke hunnunsu.

https://p.dw.com/p/3Xu5h
Zentralafrikanische Republik Parteitreffen mit Präsident Touadera
Hoto: DW/J. M. Bares

Tun farko shugaba Faustin-Archange Touadéra ya gargadi kasashen duniya da su ba shi kwarin gwiwa a game da fafutukar da yake na yakar kungiyoyin mayakan da ke dauke da makamai wadanda suka yi fatali da yarjejeniyar da aka cimma a birnin Khartum na Sudan yau shekara daya ke  nan. Marie-Noelle Koyara ministan tsaro ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta shaida wa tashar DW cewa a yanzu an samu sauyi sakamakon yadda suka samu nasarar murkushe kungiyoyin mayakan.

''Har shekarar bara ana batun kashi uku bisa hudu na kasar da ke hannun mayakan wanda garuruwa ne da ke da arzikin ma'adinai don haka ba dukka garuruwa ba ne ke cikin hannun mayakan. Kun gani yunkurin nasu na kame garuruwa masu arziki karkashin kasa wata dabara ce ta samun kudi don sayen makamai domin ci gaba da yin ayyukansu na tarzoma."

Ana samun tashe-tashen hankula Afirka ta Tsakiya duk da sojojin Majalisar Dinkin Duniya
Ana samun tashe-tashen hankula Afirka ta Tsakiya duk da sojojin Majalisar Dinkin DuniyaHoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

Ana ci gaba da samun tashin hankalin a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyyar duk da sulhun da aka cimma a bara tsakanin kungiyoyin mayakan da gwamnati a Sudan, inda aka rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya, wacce ta tanadi kwance damar mayakan. Kawo yanzu daga cikin kungiyoyi mayakan 14, 11 sun ajiye makamai sai uku wanda ake fatan nan gaba za su ajiye makaman a cewar ministan tsaron ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

"A kan wannan hanya ta neman tattaunawa, kasashen duniya da dama na dafa mana. Akwai ma kungiyoyin masu zaman kansu na Jamus da ke tallafa mana a game da wannan yunkuri ta hanyar kauda fitina domin sake dawo da zaman lafiya. Don haka muna kan kyakkyawar hanya mai tabbatar mana da kwarin gwiwar abin da muke yi.''

Faustin-Archange Toudera da Vladimir Putin lokacin wata ganawa a St. Petersburg
Faustin-Archange Toudera da Vladimir Putin lokacin wata ganawa a St. PetersburgHoto: Imago/TASS/Russian Presidential Press and Information Office/M. Klimentyev

A karon farko Rasha za ta bai wa kasar Afirka makamai a karkashin wata yarjejeniya da aka cimma  ta fuskar harkokin tsaro, wani abin da ake ganin sabon abu, sai dai ministar ta ce sun dade suna hulda da Rasha.

"Rasha zan gaya muku cewar tana kasarmu tun a shekara ta 1964, wato tun zamani Tarayyar Sobiet  ba su taba tafiya suka bar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya har zuwa yau ba. Muna da shirin horo na sojojinmu. Babu daya daga cikin kasashen Turai wadanda suka amince su taimaka mana da makamai saboda ka'idojojin kungiyar Tarrayar Turai, ba su ba da izini ba, amma a karshe shugaban kasarmu ya samu amincewar kasar Rasha kan ba mu tallafi na makamai a cikin rundunonin sojojinmu."

 Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai ta samu kanta cikin wani hali na tashin hankali tun a shekara ta 2013 lokacin da wani kawancen kungiyoyin mayaka suka kifar da gwamnatin François Bozizé. A halin yanzu dai sannu a hankali tattalin arzikin kasar na farfadowa, wanda bankin duniya ya ce a shekara ta 2019 kasar ta samu habakar tattalin arziki da kashi 4,8 cikin 100. A bana ake shirin sake gudanar da zaben shugaban kasa a kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.