1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Afirka ta Kudu ta garkame iyakarta da Mozambik

November 6, 2024

Afirka ta Kudu ta rufe iyakarta da Mozambik sakamakon zaman zullumi da kuma tashin hankali da ake ciki a kasar bayan sanar da 'dan takarar jam'iyyar FRELIMO a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.

https://p.dw.com/p/4mgen
Yan sanda na kokarin murkushe masu zanga-zanga a Mozambique
Yan sanda na kokarin murkushe masu zanga-zanga a MozambiqueHoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Hukumar da ke kula da iyakokin Afirka ta Kudu ta sanar da cewa ta samu rahotannin kai wa wasu motoci farmaki a yankin gabar ruwa na Lebombo da ke kan iyakar kasar da Mozambique, wanda hakan ya sanya ta daukar wannan mataki domin dakile bazuwar tashin hankalin Mozambik zuwa cikin kasarta.

Karin bayani: 'Yan bindiga a Mozambik sun halaka manyan 'yan adawar gwamnati 

Matakin na zuwa a daidai lokacin da gamayyar jam'iyyun adawa suka kira zanga-zangar gama-gari a Alhamis 7 ga watan Nuwambar 2024, domin kalubalantar nasarar Daniel Chapo na jam'iyyar FRELIMO, wacce ta shafe shekaru da dama ta na sharafinta a siyasar kasar ta Mozambik.