1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Allurar corona a Afirka ta dauki hankali

Zainab Mohammed Abubakar LMJ
January 28, 2022

Samar da riga-kafin corona a Afirka ada takunkumin ECOWAS kan Mali da kuma gasar AFCON, sun dauki hankulan jaridun Jamus na wannan makon.

https://p.dw.com/p/46FDB
Hoton sirinji dauke da allurar riga-kafin corona
Kokarin samar da kamfanin yin alluran riga-kafin corona a Afirka ta KuduHoto: Fleig/Eibner-Pressefoto/picture alliance

A sharhin jaridar Die Welt ta rubuta mai taken "Daga yanzu Afirka ba za ta sake rokon allurar riga-kafi ba". Tsawon lokaci dai nahiyar na dogaro ne da magungunan da take samu daga kasashe masu ci-gaban masana'antu. Wani masanin kimiyyar harhada magunguna Partrick Soon-Shiong da ke zaman hamshakin mai kudi wanda a kullum yake da abin yi, na fatan sauya dogaro da kasashen ketaren. Haifafen kasar Afrika ta Kudu, iyayen Soon-Shiong 'yan ci-rani ne na kasar Chaina kuma ya taso a lokacin da ake mulkin nuna wariyar launin fata watau Apateheid. A ranar Laraba da ta gabata ne dai yayin bikin bude masana'anta da cibiyar bincike ta NantSA a birnin Cape Town, ya sanar da fara sarrafa alluran riga-kafin domin nahiyar da ma fitarwa zuwa ketare. Ya yi alkawarin zuba tsabar kudi Euro miliyan 170 cikin shirin da zai gudana tare da hadin gwiwar jami'o'i uku na Afirka ta Kudu da wasu cibiyoyin bincike. Sarrafa alluran riga-kafin a cewar hamshakin dan kasuwar, zai sa nahiyar Afirka ta yi bankwana da dogaro kan kasashe masu ci-gaban masana'antu kuma NantSA zai kasance kamfani mafi girma a duniya kana ya samar da ayyukan yi.

Ghana Accra | Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma | ECOWAS
Mali na ci gaba da fuskantar takunkumai daga ECOWAS ko CEDEAOHoto: IVORY COAST PRESIDENTIAL PRESS SERVICE/REUTERS

"Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma na ci gaba da kakabawa Mali takunkumi, sai dai hakan bai jefa al'umma cikin fargaba ba kasancewar akwai gibin da ke ba su mafita". Da haka ne jaridar Die Tageszeitung ta bude sharhin da ta wallafa game da halin da al'ummar wannan kasa ta yankin yammacin Afirka, suka tsinci kansu tun bayan juyin mulkin baya-bayan nan. Tun a 'yan kwanakin da suka gabata ne dai aka rufe kan iyakokin kasar ta Mali, a wani bangare na takunkumin da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO din ta kakabawa kasar. A taron da ta gudanar ranar Lahadi, kungiyar ta gabatar da wasu tsauraran matakai a kan gwamnatin soja ta Assimi Goita. Baya ga rufe kan iyakar, takunkumin ya kuma hada da rike duk kadarorin da Malin take da su a babban bankin yankin yammacin Afirka da duk wasu harkokin kasuwanci. To sai dai masana tattalin arzikin yankin sun yi gargadin illar da wadannan matakai kan haifar, musamman ga kasashe makwabta. Ga misali Malin da ke amfani da tashar jirgin ruwa ta Senegal, ta fi muhimmanci ga Dakar a kan dukkan kasasshen Turai gaba daya. Don haka rattaba hannu kan takunkumin da shugaba Macky Sall ya yi, tamkar ya sayi wukar yanka kansa ne.

Kwallon Kafa - 2021 Gasar cin kofin kwallon kafa na kasashen Afirka - Kamerun
Gasar cin kofin kwallon kafa na kasashen Afirka AFCONHoto: Alain Guy Suffo/empics/picture alliance

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung labari ta buga game da gasar cin kofin Afirka da ke gudana a kasar Kamaru mai taken "Mai mulkin mallaka da wasanninsa." Jaridar ta ci gaba da cewa ana gudanar da gasar cin kofin Afrika a Kamaru, gwamnati shugaba Paul Biya mai salon sai Mahdi ka ture na fatan samun labarai masu kyau. Shin zai bayyana kuwa, mai shekaru 88 da haihuwar da cikin shekaru 40 na mulkinsa ya gwamnaci zama a dakunan otel a birnin Geneva na kasar Switzerland maimakon a kasar da yake mulki? Wannan na daya daga cikin tambayoyin da jama'a suka rikayi wa kansu lokacin fara wasan na AFCON a farkon watan Janairun da muke ciki. Paul Biya ya zo filin wasan cikin motar alfarma, yana dagawa  mutane hannu. Daga nan ne Kamaru ta doke Burkina Faso da da ci biyu da daya. Nasarar da ake dangantawa da zuwan shugaban kasar na bai wa 'yan wasan kwarin gwiwa. Gasar cin kofin Afirka, ita ce gasar wasanni mafi muhimmanci a nahiyar. Kungiyoyi 24 ne ke wasa, wadanda aka fi so su ne Aljeriya da Masar da Senegal. Kusan mutane biliyan daya ne ke kallon wasan daga sassan duniya. Ga Kamaru mai masaukin baki da shugabanta ya tsufa ba batun kwallon kafa ba ne kawai, batu ne na sake ceto martabatar kasar da ke cikin wadi na tsaka mai wuya.