Sharhin jaridun Jamus kan Afirka
September 4, 2020A labarin da ta buga na halin da ake ciki a Malin, jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa ta yi, kasashe makwabtan Mali sun rasa gane irin matakin da za su dauka a kanta. Ta ce Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar da ke shugabantar kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Yankin Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO, ya fito fili ya ce ba za su yi sassauci ba matukar sojojin Malin ba su mika ragamar mulki ga gwamnatin farar hula ba. Sannan ta bukaci a shirya zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki cikin watanni 12 masu zuwa.
Ta kara da cewa juyin mulki wani mummunan ciwo ne da maganinsa guda daya ne wato takunkumi. ko da yake sojojin sun saki hambararren shugaban kasa Ibrahim Bobacar Keita da yanzu haka yake fama da rashin lafiya, amma sun yi fatali da kurarin na Ecowas, kuma bisa ga dukkan alamu babu wani mataki da ECOWAS ko CEDEAO din za ta iya dauka a kansu, lamarin da ke nuni da gazawar kungiyar da ke da kasashe 15 a matsayin mambobinta.
Daga rikicin Mali sai bikin sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Sudan da 'yan tawaye, inda a nan ma jaridar ta Frankfuter Allgemeine Zeitung ce ta yi tsokaci tana mai cewa: A farkon wannan mako ne a birnin Juba na kasar Sudan ta Kudu, kungiyoyin 'yan tawayen Sudan guda biyar sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin birnin Khartoum, bayan kwashe tsawon shekara guda sabuwar gwamnatin Sudan din tana tattaunawa da 'yan tawayen. Sau da dama dai ana dakatar da tattaunawar sakamakon fadace-fadace da suka rika kunno kai a sassa dabam-dabam na kasar.
Bayan cimma yarjejeniyar da shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya jagoranci bikin sanya mata hannu a birnin Juba, Firaminista Abdalla Hamdok na Sudan ya yi kira ga kungiyoyin 'yan tawayen da su ajiye makamansu kuma su je birnin Khartoum domin ci gaba da shawarwari, bisa manufar cimma tsagaita wuta mai dorewa da duba batun bai wa yankunan 'yan tawaye da ke yammaci da kudancin kasar 'yancin cin gashin kai. Sai dai ayar tambaya a nan ita ce ko yarjejeniyar za ta dore musamman ma a lardin Darfur, inda a baya-bayan nan hare-haren da 'yan bindiga ke kai wa mazauna kauyuka suka karu, abin da kuma ya yi sanadi na tserewar mutane kimann dubu 10?
Ba kudin sabulu bare na maganin kashe kwayar cuta. Wannan shi ne taken labarin da jaridar Die Tagsezeitung ta buga, tana mai mayar da hankali kan annobar coronavirus a kasar Yuganda. Ta ce a kasar ta Yuganda kamar a sauran kasashe masu tasowa, annobar coronavirus ta kara gurgunta harkar bayar da ilimi, inda tun bayan sanya dokar kulle miliyoyin yara 'yan makaranta ba sa zuwa makaranta ballantana ma su sami abinci kyauta da ake ba su a makarantun gwamnati. Jaridar ta ce su ma makarantu masu zaman kansu, na gwagwarmayar yadda za su ci gaba da wanzuwa. Koma bayan harkokin kasuwanci ya sa da kyar magidanta ke samun abin sakawa a bakin salati, ba a ma batun sayen kayan kariya na annobar cutar ta corona.