Afghanistan tsakanin nuna tirjiya da saduda
Bayan Taliban ta kwace madafun iko, mutanen Afghanistan na kokarin fita daga kasar. Amma akwai masu nuna tirjiya. 'Yan Afghanistan da dama sun fito kan tituna zanga-zangar adawa da tsagerun masu kaifin kishin Islama.
Zanga-zangar ranar tunawa da samun 'yanci
Bayan jin girgiza tun farko, mutane daga bangarorin Afghanistan sun fito kan tituna suna zanga-zangar adawa da gwamnatin Taliban. Ranar 19 ga watan Agusta da kasar ta yi bikin ranar samun 'yanci, mutane a Kabul da gabashin Afghanistan sun fito tituna suna murnar shekaru 102 da kawo karshen mulkin mallaka na Birtaniya. Suna rike da tutocin kasar da nuna adawa da sake dawowar kungiyar Taliban.
Amfani da tuta kan hadin kai
Tutar Afghanistan mai launikan baki, da ja da kuma kore babbar alama ce a zanga-zangar ranar tunawa da samun 'yanci, launikan da suka bambanta da tutar Taliban mai launin fari. Daya daga cikin daruruwan masu zanga-zangar ya ce fitowa da makwabtansa da sauran jama'a suka yi kan adawa da Taliban ya karfafa masa gwiwa.
Nasara kan dakarun kasashen ketare
Mayakan Taliban da masu goya musu baya sun fito kan tituna saboda murnar tunawa da ranar samun 'yanci, yayin da mayakan ke cewa sun yi nasara kan Amirka. Ba su fito da tuta mai launikan baki, da ja da kuma kore ba, amma tutarsu.
Tutar Taliban: Fari da baki
Fitowa da farin tuta na nufin mika wuya a Afghanistan, alama ce Taliban ta sake dawowa kan madafun iko. Suna nufin mika wuya da addini. Mayakan tsageru sun bazama kan tituna na Afghanistan inda suke sintiri.
Tsallake kan iyakar kasashe makwabta
'Yan Afghanistan da dama na neman tserewa daga kasar tun lokacin da Taliban ta sake kwace madafun iko. Wata daga cikin hanyar ita ce iyaka da Pakistan. Iyalan da ke wannan hoton sun tsere.
Tsira ta kowane hali
Dafifin 'yan Afghanistan ranar Jumma'a (20.08.2021) a birnin Kabul suna jira domin shiga jirgin saman sojan Amirka. A filin jirgin saman Hamid Karzai da ke birnin ana zaman tararrabi. 'Yan Taliban na kokarin hana mutane zuwa filin jirgin saman, yayin da dakarun Amirka ke tabbatar da doka. Mutane da dama sun mutu sakamakon yamutsi.
Abin da aka bari a baya
Mutanen da suka tsallake shingen binciken Taliban kan titunan birnin Kabul suna barin motocinsu a filin jirgin saman, bisa tunanin za su tsere daga kasar. Mutanen da suka gaza shiga filin jirgin saman sun lalata motocin.
Kwashe mutane a yanayi mai tsauri
Sojojin Amirka na kokarin samar da yanayin tsaro a filin jirgin saman birnin Kabul. Amirka da sauran kasashen Yammacin Duniya suna fuskantar suka kan rashin kwashe 'yan kasashensu da 'yan Afghanistan da suka yi aiki tare cikin lokaci. Yanzu babu tabbacin mutane da suke fuskantar tsangwama da suka hada da 'yan jarida na Afghanistan za su iya ficewa zuwa tudun mun tsira.
Hari a filin jirgin saman Kabul
Gomman mutane ne farar hula da sojojin Amirka suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai filin jirgin saman birnin Kabul ranar 26.08.2021. Kungiyar IS ta dauki alhakin kai harin. A hoton da ke sama ana kokarin daukar wadanda suka ji rauni zuwa asibiti.