1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfghanistan

Afghanistan: Girgizar kasa ta kashe sama da mutum 2000

October 8, 2023

Sabbin alkaluman da gwamnatin Taliban ta fitar kan girgizar kasar da ta auku a Afghanistan na nuni da cewa ibtila'in ya yi ajalin sama da mutum 2.000 tare da jikkata wadansu gommai.

https://p.dw.com/p/4XGPD
Girgizar kasa ta kashe sama da mutum 2000 a AfghanistanHoto: Omid Haqjoo/AP/picture alliance

A lokacin da yake sanar da wadanan alkaluma kakakin gwamnatin ta Taliban Zabihullah Mujahid ya ce girgizar kasar mai karfi maki 6,3 a ma'aunin rishter ta ritsa da rayukan mutane 2.053, kana kuma mutane 1.240 sun jikkata yayin da gidaje 1.320 suka ruguje a kauyuka 13 na lardin Herat inda munmunan ibtila'in ya auku.

Karin bayani: Girgizar kasa ta kashe gomman mutane a Afghanistan

To sai dai a cikin wata sanarwa hukumar Lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa adadin wadanda suka mutu da yanzu na iya karuwa mudin ba a ci gaba da aikin ceto ba.

Wannan ibtila'i dai ya zo wa Afghanistan ne a daidai lokacin da kungiyoyi da kasashen duniya suka mayar da kasar saniyar ware sakamakon takun saka da suka shiga da gwamnati mai tsatsauran ra'ayi ta Taliban bayan zuwanta kan madafun iko.