1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Namibiya: Adawa da yarjejeniyar kisan kiyashi

Mouhamadou Awal Balarabe RGB
January 23, 2023

Wani lauya na kasar Namibiya ya shigar da kara kotu domin kalubalantar yarjejeniyar da Jamus ta amince da kisan kiyashin da aka yi wa 'yan kabilar Herero da Nama.

https://p.dw.com/p/4MaVa
Hoto: Getty Images/S. Gallup

Wani lauya na kasar Namibiya ya shigar da kara kotu domin kalubalantar yarjejeniyar da Jamus ta amince da kisan kiyashin da aka yi wa Herero da Nama. Tashar DW ta samu takardun korafin da ya shigar wanda bisa ga dukkanin alamu ke takaita ikon gwamnatocin biyu. 

Duk da cewa ana danganta shi da lauyan da ya fi shahara a Namibiya, amma a wannan karon Barista Patrick Kauta ya debo da zafi saboda yana tinkarar masu fada a ji a kasarsa. Hasali ma shari'a da ake wa lakabi da "Bernadus Swartbooi vs. Shugaban majalisar dokoki" ta shafi shugaban kasa da shugaban gwamnati da kakakin majalisa da majalisar dokoki da kuma babban mai shigar da kara na kasar. A karar da ya shigar, ya yi da'awar cewar: "yarjejeniyar hadin gwiwa" da Jamus da Namibiya suka rattaba hannu a kai a kan kisan kiyashin da aka yi wa 'yan kabilar Herero da Nama tsakanin 1904 zuwa 1908 ya saba wa doka.

Tun a shekara ta 2021 ne dai aka cimma wannan yarjejeniya, amma har yanzu gwamnatin Namibiya ba ta sanya hannu a kanta ba. A karon farko a hukumance dai Jamus ta nemi afuwar kisan kiyashin da aka yi, tare da alkawarin bayar da tallafin ayyukan raya kasa a yankunan Herero da Nama na Euro biliyan 1.1 na tsawon shekaru 30. Sai dai wani dan siyasa mai kwarjini kuma dan adawa Bernadus Swartbooi da sarakunan gargajiya 11 na kabilun Herero da Nama ne suka shigar da kara kotu, domin yin watsi da kakkausar murya da yarjejeniyar, yayin da sauran wakilan al'umma ke goyon bayanta. ko da babban basarake na Herero, Mutjinde Katjiua, ya nunar da cewar dokar da majalisar Namibiya ta zartar a shekarar 2006 ya tanadi tattaunawa kai tsaye da Jamus domin tantance diyya da za ta biya.

Deutschland Rückgabe sterblicher Überreste aus Deutscher Kolonialzeit
Jamus ta amince ta biya diyya ga al'ummar Herero da NamaHoto: picture-alliance/AA/A. Hosbas

Lauyoyin sun ja hankali kan muhimman abubuwa biyu: Na farko suka ce shugaban majalisar ya katse muhawara kan yarjejeniyar a majalisar dokokin Namibiya  ba bisa ka'ida ba. A nasu ra'ayin dai, yarjejeniyar bian diyya na Euro biliyan 1.1 ga Namibiya ya sabawa doka. Sai dai masaniyar shari'ar kasa da kasa ta Jamus Karina Theurer ta shawarci sassa biyu da raja'a kan tsarin shari'ar Namibiya saboda yana kwatanta adalci.

Sai dai yunkurin da kabilun Herero da Nama suka yi a baya ta hanyar shigar da kara a wata kotun Amirka a shekarar 2017 na neman diyya daga Jamus ya ci tura. Da alama dai gwamnatin Namibiya za ta dukufa ka'in da na'in wajen kare matsayinta a kan wannan yarjejeniya. Ko da 'yan kwanakin baya, gwamnatin ta nunar da cewa lauyan da ke kalubalantar yarjejeniyar ba shi da masaniya game da kundin tsarin mulkin Namibiya da ikon shugaban kasa da na gwamnati. 

Wannan shari’ar dai ta jefa gwamnatocin biyu watau ta Namibiya da ta Jamus cikin wadi na tsaka mai wuya, tun ma kafin a yanke hukunci. Hasali ma dai, Jamus na son aiwatar da yarjejeniyar cikin gaggawa. Ita kuwa gwamnatin Namibiya a daya bangaren, ta dage kan biyan diyya a hukumance, kuma tana son karin kudin diyya - wanda a zahiri ba zai yiwu ba sai idan an sake tattaunawa. Ko da masani Henning Melber, sai da ya ce shari'ar ta zama kadangaren bakin tulu

A cewar Mujallar labarai ta Der Spiegel, gwamnatin tarayyar Jamus ta yi tayin biyan diyya ta Yuro biliyan 1.1 da aka alkawarta wa Namibiya a cikin kasa da shekaru 30. Amma kuma a lokaci guda kuma, ta nace cewa ya kamata a kara sanarwar hadin gwiwa, amma ba a sake tattaunawa kan kisan kiyashin da aka yi wa Herero da Nama ba.