Abubuwan da ke gaban Afirka a 2021
Corona da zabubbuka da rigingimu da tsarin kasuwanci maras shinge: Wadannan ne muhimman abubuwan da ke gaban Afirka a 2021.
Kaddamar da babban tsarin kasuwancin-bai-daya a duniya
A ranar farko ta sabuwar shekarar 2021, tattalin arzikin Afirka zai shiga wani sabon babi, za a kaddamar da tsarin kasuwanci maras shinge a Afirka (AfCFTA). Hakan zai bude kofar yin irin wannan a duniya baki daya nan da wasu shekaru. Masana sun ce AfCFTA zai habbaka arzikin Afirka amma corona za ta kawo cikas wurin aiwatar da shirin.
Rana ba ta karya a Yuganda
'Yan sanda sun ta kama 'yan adawa har abin ya kai ga wasu suka mutu. Hotunan abubuwan da suka faru a wurin yakin neman zabe na tayar da hankali kwarai. Sai dai a ranar 14.01.2021 'yan Yuganda za su zabi ko dai Yoweri Museveni da ya kwashe lokaci yana mulki ko kuma mawaki Robert Kyagulanyi da ake wa lakabi da Bobi Wine.
Shekara mara dadi ga Habasha
'Yan Habasha za su samu hadin kai bayan dirar mikiyar da gwamnati ta yi wa dakarun yankin Tigray? Ko dai kasar za ta shiga rudani saboda rikicin cikin gida da ya yi mata kawanya? Shekarar 2021 za ta tabbatar ko Firaminista Abiy zai iya tsaftace dimukuradiyya a azben da ake sa ran yi a watan Mayu ko Yuni a kasar.
Matsalar 'yan gudun hijira
Rikicin yankin Tigray ya kori daruruwan mutanen Habasha zuwa Sudan wace ita ma ke da matsaloli. Ana zullumin irin wannan zai haifar da sabbin matsalolin 'yan gudun hijira a 2021 kuma babu alamun magance wadanda ake da su a kasashe irinsu Kamaru da arewacin Najeriya da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo.
Zabuka masu hatsari na tafe
Ba wai a Uganda da Habasha kadai ba, akwai zabe a Benin da Somaliya da Sudan ta Kudu da Zambiya da Cape Verde da Chadi da kuma Gambiya inda 'yan kasa za su zabi shugabanninsu a 2021. Ana hasashen kwashewa lafiya a wasu kasashen, amma a Somaliya da Sudan ta Kudu an fara ganin alamomin tashin hankali.
Fatan samun rigakafin corona
Duk cewa corona ba ta yi wa Afirka katutu kamar yadda aka yi hasashe ba, amma tasirin cutar ya bar 'tabo' a fannin tattalin arziki da kiwon lafiya. Ana fatan samun rigakafi, amma Afirka ba ta shirya ''gangamin samun gagarumin rigakafi irin wannan ba'' acewar Matshidiso Moeti na hukumar WHO. Ana tunanin sai a tsakiyar 2021 za a fara rigakafin coronavirus a Afirka.
Akwai yiwuwar a yafe basussuka?
Ko dai da an kawo rigakafin corona, zullumin talaucewar kasashen Afirka na nan. Duk da dai kasashen G20 sun fito da tsrain yafe wa wasu kasashe basussuka a farkon zuwan corona, amma kungiyoyi na kira ga gwamnatocin Afirka da su rage basussukan da suke karbowa daga waje domin takaita tasirin zuwan corona ga arzikinsu.
Matsalar sauyin yanayi na kunno kai
Rashin ruwan sama da farin-dango ga kuma ambaliyar ruwa: Babu nahiyar da ta dandana illar sauyin yanayi kamar Afirka. Sai dai matasa kamar Vanessa Nakate 'yar Uganda na son a daina maganar fatar-baki, tana son duniya ta ji kukan Afirka kan sauyin yanayi musamman a taron sauyin yanayi da aka tsara gudanarwa a Nuwamba 2021.