Abiy ya ki tattaunawa da 'yan Tigray
November 27, 2020Talla
Abiy ya yi wannan bayanin ne a lokacin da ya ke ganawa da wasu wakilai uku daga Kungiyar Tarayyar Afirka, a kokarinsu na kawo karshen rikicin da ake tsoron zai iya mamaye yankin gaba daya.
Dubban mazauna Tigray ne ke ci gaba da tserewa daga yankin, bayan cikar wa'adin da Abiy Ahmed ya bai wa mayakan fafutukar da su mika wuya ko sojojin gwamnati su kai sumamen karshe na murkushe su.
Da alama dai wannan matakin bai yi wa wakilai na musamman na AU da suka hada da tsoffin shugabannin kasasahen Laberiya Ellen Johnson Sirleaf da na Mozambik da kuma na Afirka ta Kudu dadi ba.