An karrama firaministan Habasha
December 10, 2019Talla
A cikin watan Oktoba da ya gabata ne aka bayyana ba da lambar yabon ga firaministan na Habasha saboda rawar da ya taka wajen samar da zaman lafiya tsakanin kasarsa da Iritiriya bayan da aka kwashe kusan shekaru 20 ana gwabza yaki tsakanin kasashen biyu wadanda ba su ko ga maciji. A shekara ta 2018 watannin uku kawai da zuwansa a kan mulki firaminista na Habasha Abiy Ahmed ya yi wata ganawa ta tarihi da shugaban Iritiriya Isaias Afeworki, a birnin Asmara domin farfado da zaman lafiya tsakanin kasashensu biyu.