WFP: Tigray na fama da karancin abinci
August 20, 2022Kusan rabin mutanen da ke yankin Tigray da rikici ya dai-daita a Habasha na rayuwa cikin matsanancin karancin abinci, a cewar Shirin Samar da Abinci na MDD, WFP. Tun daga watan Nuwamba na shekarar 2020 yankin na Tigray ya zama fagen daga a tsakanin dakarun yankin na Tigray People's Liberation Front da kuma sojojin gwamnatin Habasha da ke karkashin firaminista Abiy Ahmed, lamarin da ya jefa al'ummar yankin cikin bukatar agaji.
A cikin sabon rahoton da WFP ya fitar, ya ce, mutanen Tigray miliyan shida ne suka rasa hanyar da za su sami abinci sannan akwai wasu karin mutane miliyan 13 da ke fama da barazanar yunwa a yankunan Afar da Amhara da ke makwabtaka da Tigray. Cikin wadanda suka bi dandana kudarsu, a cewar alkaluman na shirin na MDD, akwai mata masu juna biyu da wadanda ke shayarwa da ma kananan yara 'yan kasa da shekaru biyar da samun abinci ya zamar musu jidali.