A yau jami´an IAEA zasu tabbatar da rufe tashar nukiliya a Yongbyon
July 15, 2007Talla
Kasar Amirka ta ce KTA ta rufe tashar nukiliyarta ta Yongbyon da ake takaddama a kai. A wannan tasha dai ana iya saraffa sinadarin plutonium wanda ake harhada makaman nukiliya da shi. Wani kakakin ma´aikatar harkokin waje a birnin Washington ya nunar da cewa hukumomi a birnin Pyongyang suka sanar da gwamnatin Amirka haka. Yanzu haka dai ana jira hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta tabbatar da wannan labari. Sifetocin hukumar wadanda tun a jiya asabar suka isar kasar ta KTA a yau zasu ganewa idonsu wannan mataki na rufe tashar nukiliyar da KTA ta dauka. A tattaunawar da ake yi na kasashe 6 a cikin watan fabrairu KTA ta yi alkawarin rufe tashar ta nukiliya. Su kuma a nasu bangaren kasashen Amirka Japan Rasha China da kuma KTK su yi mata alkawarin ba ta taimakon jin kai da na tattalin arziki.